Dr. Abubakar Muhammad Isa
Wannan mawallafi dan asalin Jihar Kano ne a Najeriya. An haife shi a ranar 30/4/1983 shekarar Miladiyya
Bayan karatun allo da haddar Qur’ani mai girma a shekarar 1997, ya yi:
1. Makarantar Firamare da Sakandare a Kano.
2. Kwalejin share fagen shiga Jami’a (CAS Kano) a shekarar 2006.
3. Shaidar Karamar Diploma a kan horon Malanta da Harshen
Larabci da harkokin addinin Musulunci a shekarar 2007.
4. Digirinsa na farko a Jami’ar Bayero da ke Kano shekarar
2011,
5. Samu shaidar Kwarewa ta Malanta a Kwalejin FCE Kano a shekarar 2015
6. A shekar 2012 ya zama malami a Kwalejin Musulunci da Shari’a ta Kano
a sashen nazarin harkokin Musulunci (Islamic Studies Department).
7. Ya kammala digirinsa na biyu a Jami’ar Jazera da ke da ke qasar Sudan a
shekarar 2020.
8. Ya kammala Digirin digri-gir (Ph,D), a Jami’ar Assalam da ke
Kharthoum babban birnin qasar Sudan a shekara ta dubu biyu da ashirin
da hudu 2024. Ya zama mataimakin shugaban sashen Musulunci (Deputy
H.O.D Islamic Studies Department), a kwalejin shari’a da Musuluci ta
jahar Kano (Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies) a
shekarar 2024.
A yanzu kuma shi ne shugaban sashen addinin Musulunci a kwalegin,
(H.O.D) Islamic Studies Department.
Wasu daga shedar qwarewa ta musamman sun haxa da Ijaza ta Tajwidi
da cibiyar Al-azhar da ke Kano a shekarar 2003, da shedar haddar Qur’ani
a Jami’ar Qur’ani da ke Sudan a shekarar 2020..